DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ne ya bayyana hakan ya yin wata ganawa da manema labarai a headkwatar rudunar ta jihar Kano.
Gumel ya ce sun samar da isassun jami’an tsaro wadanda suke cikin shiri domin tabbatar da uwar gidan shugaban kasa ta kammala ziyarar da zata kawo kano lami lafiya .
Gumel ya ce rundunar ta dauki kwararan matakan tsaro domin tabbatar da ziyarar lafiya.
“Mun tattara isassun jami’ai masu dauke da makamai domin baiwa uwargidan shugaban kasa kariya kafin ziyarar, da lokacin da kuma bayan ziyarar,” in ji Gumel.
Kwamishinan ya kuma ce tuni rundunar ta fara shirin “Operation Show Force” tare da sauran jami’an tsaro domin nuna shirin su kan ziyarar uwar gidan.
Ya bayyana cewa an dauki matakan ne domin baiwa mazauna jihar damar tarbar uwargidan shugaban kasar da mukarrabanta ba tare da wata barazana ta tsaro ba .
Kwamishinan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasar jihar da su ja hankalin magoya bayansu da su nisanci duk wani nau’in tashin hankali da ‘yan daba kafin ziyarar uwargidan shugaban kasa da kuma bayan ziyarar.
Gumel ya ce: “Ba za mu amince da duk wani aiki da zai kawo rudani kafin ziyarar, lokacin da kuma bayan ziyarar ba”.












