Kwara – ‘Yan bindiga sun kai hari a daren yau a fadar Mai martaba Sarkin Koro a karamar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara.
Rahoton Daily Trust ya ce ‘yan bindigar sun harbe Mai martaba Janar Segun Aremu mai ritaya wanda shi ne Olukoron Koro.
An kashe Sarki, an dauke matarsa a garin Ekiti Miyagun ba su tsaya nan ba, sun dauke matar marigayi Janar Segun Aremu, sannan sun yi awon gaba da wasu mutane biyu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi ta sanar da aukuwar lamarin da safiyar ranar Juma’a.
Ejire-Adeyemi ta ce an aika dakaru domin ganin an cafko wadanda suka yi ta’adin.
Jawabin ‘yan sandan jihar Kwara “Muna tabbatarwa al’umma cewa za ayi bakin kokari wajen tabbatar da an yi gaggawar hukunta wadanda suka yi laifin.
An tsaurara matakai a yankin Koro, ana tattara jami’ai domin su ingnata tsaro domin tabatar da kariya ga mazaunan.











