• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Hukumar NDLEA Na Neman Tsohuwar Sarauniyar Kyau Ta Najeriya Ruwa A Jallo

aksam by aksam
January 29, 2024
Reading Time: 1 min read
0
Home TSARO
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Hukumar Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA ta bayyana cewa tana neman wata tsohuwar sarauniyar kyau ruwa a jallo.

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

Wadda ake zargin ita ce Sarauniyar Kyau ta Nijeriya ta Kungiyar Kasashen Rainon Ingila ta 2015/2016 kuma ita ce ta ƙirƙiro gidauniyar Queen Christmas Foundation.

Hukumar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce tana zargin Ms. Aderinoye Queen Christmas wadda aka fi sani da Ms. Queen Oluwadamilola da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi.

NDLEA ta ce tsohuwar sarauniyar ta kyau ta tsere daga gidanta da ke unguwar Lekki a birnin Legas a daidai lokacin da jami’an hukumar suka kai mata samame a ranar Laraba 24 ga watan Janairun 2024.

Hukumar ta ce jami’an nata sun kai samamen ne sakamakon sahihan bayanan sirri da suka samu kan cewa tana tu’ammali da miyagun ƙwayoyi.

NDLEA ta ce daga cikin abubuwan da aka gano a gidan Ms. Aderinoye sun haɗa da gram 606 na wani samfurin wiwi mai suna Canadian Loud, haka kuma an gano wani sikeli mai amfani da lantarki, da kuma ledojin saka kaya masu yawa da wata baƙar mota RAV 4 mai lamba Lagos KSF 872 GQ.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Rahoton yadda bom ya tashi da wasu a jihar Borno

Next Post

NBA ta sake shigar da bukatar Tinibu ya kori ministar saboda wasu dalilai

aksam

aksam

RelatedPosts

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya ta ayyana neman jami’inta ruwa a jallo

by Khadija Maitaya
July 24, 2026
Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa
LABARAI

Peace Corps of Nigeria Ta Yi Bikin Cika Shekaru 28 da Kafuwa

by Khadija Maitaya
July 10, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Jerin kamfanin tsaro na Amurka 10 da ‎China Ta Kakaba wa Takunkumi

by Khadija Maitaya
June 22, 2026
Rundunar  Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
TSARO

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

by aksam
June 16, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Jami’an EFCC Sun Cafke Jami’in Tsaro Kan Zargin Safarar Zinaren Naira Biliyan 4.4 A Kano

June 13, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

September 7, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media