Kayayyakin da suka haɗa da injinan yankan katako da na’urorin samar da wutar lantarki da kuɗinsu ya kai miliyoyin naira sun lalace a wata gobara da ta tashi da tsakar dare a jihar Rivers.
Gobarar dai ta tashi ne a babbar kasuwar katako da ke karamar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers, a cewar rahoton Daily Trust
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na daren ranar, biyo bayan kama wa da wuta da wani haɗi na wutar lantarki da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a kasuwar, bayan an dawo da wutar lantarki, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa wacce ta bayyana sunanta da Chioma ta koka da cewa:
“Lokacin da suka dawo da wutar lantarki ne, saboda ina zaune kusa da kasuwar, na ji wata ƙara mai ƙarfi kuma abu na gaba shi ne sai wuta ta kama, kuma tana yaɗuwa cikin sauri.
“An lalata injina da yawa, injinan yankan katako da janaretoci.
Babu ɗaya daga cikin injinan wanda bai kai N2m ko N3m. “Dukkansu sun lalace kuma ba a bar mu da komai ba.
Wannan (kasuwancin) shine kawai abin da nake yi don biyan kuɗin makarantar yarana.












