Daga Aliyu Abdullahi Dan Bala Gwarzo
Wani matashi yayi Tattaki tundaga jihar Bauchi har zuwa jihar kano domin taya gwamnan kano Murnar samun Nasara a kotu.
Matashi mai suna ubaidullahi saleh wanda a Kafi sani da Ubaidu Tilde mai shekara 30 a duniya dan asalin garin Tilden fulani dake karamar Hukumar Toro a jihar Bauchi yayo Tattaki kafa ikafa tundaga garin Tilde har izuwa garin kano domin taya gwamnan jihar kano Alhaji Abba kabir yusuf samun Nasara a kotun kolin najeriya.
Ubaidu Tilde ya bayyana cewa “nayi wannan Tattaki badan komai ba sai dan Kauna da soyayyar da nakewa gwamnan jihar kanon Inda tunbayan da aka Shiga kotu a tsakanin jamiyyar n.n.p.p da jamiyyar a.p.c nayiwa Kaina Alkawari zanyi wannan tafiya domin nataya Abba gida gida murna.”
Idan za’a iya tunawa a ranar Juma’ar data gabata 12 ga watan junairu na shekarar 2024. Ne kotun kolin najeriya ta tabbatar da Abba kabir Yusuf a matsayin hastaccen zababban Gwamnan jihar kanon












