RAMIN HAKORI DA ABUBUWAN DA KE KAWOSHI (kashi na daya)
Da yawan mutane na fama da lalurar ramin hakori musamman a irin wannan lokaci na sanyi.
wani da zaran yaci wani abu mai sanyi ko zafi kokuma zaqi sai hakorin yafara yi masa ciwo wani kuwa haka Kawai hakorin nasa ke yi masa ciwo kuma ta kan kai shi ga hakorin nasa ya yi rami ko kogo.
Ramin hakori, wanda ake kira Dental caries ko Tooth decay, a turance yana faruwa ne da farko ta hanyar haɗu war wasu abubuwa irin su
1.Kwayoyin halittu na (Bacteria): Kasancewar wasu kwayoyin cuta, kamar Streptococcus mutants shi kuma yake haifar da samuwar plaque akan hakora.
wanda wadannan kwayoyin halittu Allah yayisu ne a baki, asali basa cutar da mutum ana kiran su (normal flora) a turance amma da zaran mutum yaci abu me zaqi da zai iya makale masa a hakori, matuqar be wanke bakinshi ba yadau lokaci wadannan halittu zasuci daga wannan abun, Sanan su samar da wani camical da ake kira da (lactic acid) dayake da karfi wanda shike sabbaba ramin hakori.
Sai kuma abu na 2 da ke kawo Ramin hakorin shi Sukari wanda ake cewa (Refine carbohydrate): Cin abinci mai sikari da sitaci kamar biredi, biscuit ko alawa DSS na samar da makamashi ga kwayoyin halittun, wanda ke samar da sinadarin acid da ke zubar da elamen din hakori.
Sai abu na 3 Rashin Tsaftar Baki: Rashin wanke baki musamman bayan cin Abu mai zaki, yana ƙara haɗarin kamuwa da ramin haƙori, akalla ko kurkura baki kayi bayan shan abu Mai zaki dan ragewa kanka hadarin kamuwa da shi
Akwai bukatar wanke baki a kalla sau 2 a rana (kapin a kwanta bacci da bayan anyi karin kumallo)
Abinci da Abin sha mai dauke da acid: Abubuwan sha da abinci mai acid da yawa kamar lemon tsami na iya raunana enamel din hakori(ma’ana hakorin kanshi), yana sa haƙoran su zama masu saurin lalacewa.
Rashin samun wadataccen yawu a baki (Dry Mouth): Rashin kwararar miyau zai iya haifar da bushewar baki, wanda ke hana aikin tsaftacewa da wanke hakwara da yawu keyi.
Cigaba na tafe a kashi na biyu












