By B. Imam
Labaran Safiyar Lahadi 24/12/2023CE – 10/06/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Sojoji sun kuɓutar da mutum 52 da aka yi garkuwa da su a jihar Sokoto.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce ko sisi ba zai biya basukan ciyamomi ba har sai Kotun Koli ta umarce shi.
Dan Majalisa mai wakiltar Tsafe ta yamma a jihar Zamfara ya koka Kan yadda yan bindiga suka addabi yankin sa.
Majalisar Dokokin jihar Kogi sun zabi mace ta farko a tarihi a mataimakiyar kakakin Majalisar jihar dan maye gurbin wanda yayi murabus.
Hukumar kula da gidan yari tace masu jiran a zartas masu da hukuncin kisa sun kai mutum dubu 3,413.
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gwangwaje ‘yan Majalisar jihar da kuma Alkalai motocin alfarma.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, gwamnoni da manyan masu fada aji sun halarci daurin auren dan tsohon shugaban kasa Sani Abacha jiya asabar a Maiduguri.
Ɓangarorin da ke rikici da juna a Yemen sun amince da buƙatar tsagaita wuta.
Harin ƴan tawaye ya kashe fararen hula 20 a Burundi.
Jirgi mara matuki ya kai wa jirgin ruwan dakon kaya mai alaka da Isra’ila hari a tekun Indiya.
RSF ta maka Isra’ila gaban kotun ICC kan kashe ‘Yan Jarida a Gaza.
Arsenal ta tuntuɓi wakilan Ivan Toney a shirin da take yi na cinikin ɗan wasan na Brentford.
Kylian Mbappe ba ya son barin PSG a watan Janairu duk da cewa kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar nan.
EPL: Arsenal da Liverpool sun tashi 1:1 a wasan jiya.
Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Lecce da ci 2:0 a wasan jiya.
Seria A: Juventus ta sami nasara akan Frosinone da ci 2:1 a wasan jiya.










