DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
An rantsar da Sanatan ne a farkon zaman majalisar na ranar Laraba, a wani takaitaccen biki da akawun majalisar ya shirya.
Sabon Sanatan wanda lauya ne kuma shugaban majalisar dokokin jihar Plateau wa’adi biyu, ya rike mukamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi na gwamnatin shugaba Tinubu.
Lalong ya mika takardar murabus dinsa ne ga shugaban kasar a kebe bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi a ranar Larabar da ta gabata.
Idan za a iya tunawa, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, a ranar 7 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da cewa Sanata Lalong, ne ya lashe zaben.











