Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto wasu mutanen da ‘yan ta’adda suka sace tsawon shekaru 10 zuwa yanzu
Mutanen da akalla yawan su ya kai 386 kuma akasarisu mata da kananan yara sojoji suka ceto a dajin Sambisa shekaru goma bayan sace su.
Mukaddashin GOC na shiyya ta 7 a rundunar soji, AGL Haruna ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a dajin Sambisa a karamar hukumar Konduga bayan tarbar sojojin da suka gudanar da aikin na kwanaki 10
An bayyana sabon aikin da sojojin suka fara domin tabbatar da sun kakkabe dajin Sambisa daga masu aikata ta’addanci
Jihohin Arewa maso Gabas na fuskantar matsalolin da suka shafi tsaro, musamman aikin ta’addancin Boko Haram da ISWAP











