• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

‎Yau Shekara 18 Da Rasuwar Sheikh Ja’afar Mahmud Adam  

aksam by aksam
April 13, 2025
Reading Time: 4 mins read
0
Home Addini
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Innalillahi Wa’inna Ilaihirrajun!!! Mu Na Mika Sakon Ta’aziyyarmu Ga ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Na Wannan Babban Rashin

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

Daga Hassan Umar Gwammaja

Yau ake cika shekara 18 da wasu ’yan bindiga suka yi wa shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, kisan gilla a yayin da yake limancin Sallar Asuba.

‎A safiyar Juma’a, 13 ga Afrilu, 2007, wasu mahara suka kutsa cikin masallacin da ke gidan Sheikh Ja’afar a unguwar Dorayi da ke Kano, suka harbe shi a kirji, a yayin da yake sujjada, wanda hakan ya yi ajalinsa.

‎Kararuttukan Sheikh Ja’afar, musamman na Tafsirin Al-Kur’ani, sun yadu a sassan duniya, kuma har yanzu yana samun yabo game da zurfin iliminsa da iya bayani a saukake gami da amfani da kyawawan lafazin da kuma iya mu’amala.

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya kasance babban abin koyi musamman ga dalibai da malamai musamman ganin yadda ba ya shakkar tsage gaskiya cikin hikima tare da amfani da hujjoji masu gamsarwa da bayani mai warkarwa da kwararan misalai.

‎Malam bai bar shugabanni ba, bai bar masu sarautar gargajiya ba, haka kuma bai bar ma’aikatan gwamnati ba, bai bar ’yan kasuwa ba, kamar yadda bai bar talaka ba.

‎Idan mai mulki ya kauce wa gaskiya, balo- balo zai fito ya fayyace masa illar haka. Ya yi yaki da azzaluman duniya, ya fayyace fari daga baki.

Ya sassaita tunanin al’umma da hasken iliminsa kuma kararuttukansa na da farin jini har yanzu, shekara 16 bayan ya koma ga Mahaliccinsa.

‎Malam ya rasu ne a wani lokaci da al’ummar Musulmi take matukar bukatar muhimmin malami irinsa.

‎Mutum ne shi da ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen karatu da karantarwa, fadaka da fadakarwa, ankara da ankararwa.

A lokacin da mafi yawan malaman addini suka zama makwadaita, shi Malam Ja’afar sai ya zama daban, ya kasance wanda ya san kansa kuma ya rike mutuncin kansa.

‎A lokacin da wadansu malaman suka siffantu da karkatar da mabiyansu saboda neman girma da neman abin duniya, Malam Ja’afar ya kasance kaifi daya.

‎Ya dora koyarwarsa bisa turba daya, wato bisa hujja mai inganci ta Alkur’ani da Hadisi da Ijma’in Malaman Sunnah magabata.

‎Wannan hali ne ya ba shi damar kasancewa jajirtacce, wanda ba ya kyuya ko kasala.

‎A kullum yana cikin nazari da bincike kuma ba ya furta wata fatawa ba ya ambata kowane karatu, face yana da hujja da kwakkwarar madoga

‎Idan gaskiya ta zo, ba ya shayin fadinta, ya alla ga ’yan Izala ko ga ’yan Shi’a ko ga ’yan Darika ko kuma ga Kirista da ma wadanda ba su da addini.

‎A lokacin da ya fara ganin take-taken marigayi shugaban ’yan Boko Haram, Malam Muhammad Yusuf, Sheikh Ja’afar ya yi iyaka kokarinsa wajen fadakar da shi, game da fitinar da yake neman kunnowa ga al’umma.

‎Amma Muhammad Yusuf ya yi kunnen uwar shegu da hudubar Ja’afar, sai ga shi kuwa abin da ya hango ya tabbata. A yau Kungiyar Boko Haram ta zama annoba ga al’umma.

Marigayi Sheikh Ja’afar ya haifar da sauyi mai girma ga al’umma, musamman ma ga matasa maza da mata, inda suka fahimci tsantsar abin da Musulunci ke koyarwa.

‎Ta hanyar wa’azozinsa, al’umma sun karu sosai da nagartaccen ilimi kuma ana ci gaba daatasa sun fahimci tsantsar abin da ake nufi da rayuwa, sun gane tasirin neman ilimi, sun gane tasirin neman aiki ko sana’a, kamar yadda suka gane illar zaman kashe wando

‎Idan mai mulki ya kauce wa gaskiya, balo-balo zai fito ya fayyace masa illar haka; Ya yi yaki da azzaluman duniya, ya fayyace fari daga baki.

‎Wani abin takaici shi ne, har zuwa yau shekara 16 da kisan gillar da aka yi wa Malam, babu wani da aka kama daga cikin wadanda suka gudanar da aika-aikar.

‎Tarihin Sheikh Ja’afar Mahmud

Malam Ja’afar Mahmud Adam an haife shi ne a ranar 12 ga Fabrairun 1960, a garin Daura ta Jihar Katsina.

‎Ya samu gurbin karatun gaba da firamare a 1984, inda ya shiga Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnati da ke (GTC) Gwale, wacce a yanzu ake kiranta da Kwalejin Larabci ta Gwamnati (GAC), Gwale.

‎Ya kammala a 1988, daga nan ya samu gurbin ci gaba da karatu a Jami’ar Musulunci ta Madina a Saudiyya.

‎Ya yi karatunsa a can na tsawon shekara hudu, inda ya kammala a 1993.

Marigayi Malam Ja’afar ya kasance: “Ina-ka-fito-nazari, Ina-za-ka-da’awa.”

‎Gaba dayan rayuwarsa ta kasance a hidimar Musulunci.

‎Muna rokon Allah Ya jikansa da gafara, Ya amshi shahadarsa, Ya ci gaba raya ayyukansa a fadin duniya.

Allah Ya yi masa sakayyar zaluncin da aka shuka masa, Ya tona asirin makasansa da duk wadanda suka ba da goyon bayan haka ta tabbata.

‎Allah Ka tada mana da magajinsa, wanda zai ci gaba da haskaka addininKa ga al’umma.

‎Malam Ja’afar Adam, muna tuna ka, muna yi maka addu’a a kullum. Allah Ya jikanka!

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Najeriya Ta Hana A Shigo Mata Da Kayayyakin Kasuwancin ƙasar Amurka

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Kona Masallacin Juma’a, Asibiti Da Gidaje A Jihar Zamfara 

aksam

aksam

RelatedPosts

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana
Addini

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

by aksam
June 5, 2026
Innalillahi Wa’inna Ilaihirrajun!!!  Mu Na Mika Sakon Ta’aziyyarmu Ga ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Na Wannan Babban Rashin
Addini

Innalillahi Wa’inna Ilaihirrajun!!! Mu Na Mika Sakon Ta’aziyyarmu Ga ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Na Wannan Babban Rashin

by aksam
June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings
Addini

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

by aksam
June 1, 2026
Da dumi-dumi: Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ta Fitar Da Sabowar Sanarwa Akan Ganin Watan Zul-Hijja 1477 AH.
Addini

Da dumi-dumi: Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ta Fitar Da Sabowar Sanarwa Akan Ganin Watan Zul-Hijja 1477 AH.

by aksam
May 18, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Shugaba Tinubu Ya Faɗi Babban Haɗari guda 1 tak da Ke Tunkaro Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Faɗi Babban Haɗari guda 1 tak da Ke Tunkaro Najeriya

January 6, 2024
Kwace jiragen shugaba Tinibu, gwamnatin tarayya ta magantu

Kwace jiragen shugaba Tinibu, gwamnatin tarayya ta magantu

August 16, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media