Wani matashi mai suna Nurudeen Shehu, dan shekaru 37, ya hadu da ajalinsa ta hanyar rataye kansa har lahira a wata makaranta da ya ke aikin gadi a Kano
An ruwaito cewa, Shehu ya samu labarin tsohuwar matarsa ta yi wani sabon aure, lamarin da ya ja ya dauki wannan mumunan hukuncin a hannun sa
Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta jami’in hulda da jama’ar ta tabbatar da faruwar hakan a ranar Talata, inda kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ce an yi wa matashin sutura
“A ranar 28 ga watan Janairu da misalin karfe 10:30 na safe, Abdullahi Abdulsalam na Rijiyar Zaki ya ba mu rahoton cewa sun samu gawar Shehu a rataye a cikin aji.
“Yan sanda daga sashin Gwale, sun garzaya da gawar zuwa asibitin Murtala, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa, sannan aka mika gawarsa ga iyalansa don yi masa sutura.”
Jaridar Tribune Online ta tattaro cewa, labarin auren tsohuwar matarsa ne ya ja Shehu ya dauki wannan mumunan hukuncin na daukar ransa da kansa.
Gumel ya yi alkawarin cewa rundunar ‘yan sandan za ta gudanar da cikakken bincike domin gano al’amuran da suka haifar da hakan.











