Daga Hassan Umar Gwammaja
Sun gudanar da wani gangami domin nuna damuwar su kan matsalar rashin kyan hanyoyi da suke fama dasu a yankunan su.
Ɗaruruwan mazauna unguwar ta Gayawa da kewaye ne dai suka fito a ranar Asabar, din nan tare da neman ɗaukin mahukunta, kan su gyara musu titunan yankunan su da suka haɗar da na Gayawa, da titin Badaru, da na gadar Getsi, da titin na Tsahare, da kuma Jaba, da na Rimin Keɓe.
Da yake zantawa da manema labarai jagoran mutanen da suka fito gangamin mai suna Haruna Musa Isma’il, ya ce sun fito ne domin sanar da gwamnatin jihar Kano, da dukkanin shugabanninn yankunan su matsalar rashin hanyoyin da ta daɗe tana damun su shekara da shekaru.
A cewar sa, “Mun daɗe muna bibiyar mahukunta halin da muke ciki amma kawo yanzu ba’a share mana hawayen mu ba a don haka ne ma muka fito domin mu nusartar da gwamnatin halin da muke ciki don a kawo mana ɗauki, “in ji Haruna Musa”.
Anasa ɓangaren wani matuƙin baburin Adai-dai Sahu a yankin, ya shaidawa Dala FM Kano, cewa har mata biyu ne suka taɓa Haihuwa a cikin baburi ɗin sa, lokacin da zai kai su Asibiti, bisa rashin kyan hanya.
“Baya ga batun rashin kyan hanyoyi da muke fama dasu akwai kuma rashin Kwalabati da yake damun mu, wanda ida akayi ruwan sama yake shiga cikin gidajen jama’a, “in ji shi”.
Al’ummar unguwar ta Gayawa da kewaye da ke ƙaramar hukumar Ungog a jihar Kano, sun kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da shugabannin su na ƙaramar hukumar tasu, da su kawo musu ɗauki wajen gyara musu hanyoyin su da suka lalace, bisa yadda suke matuƙar shan wahala.











