• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda Hadarin mota ya halaka fiye da mutane 42

aksam by aksam
March 29, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ma’aikatar sufuri a Afirka ta Kudu ta sanar cewa wata motar bas ta fado daga wata gada kuma ta kama wuta ranar Alhamis, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 45 daga cikin 46 da ke cikin bas din.

WASHINGTON DC —
Wani yaro dan shekara takwas kadai ne ya tsira kuma an kai shi asibiti da munanan raunuka.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Motar ta taso ne daga makwabciyarta Botswana zuwa Moria a arewacin kasar, in ji wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar.

Bus plunges off cliff
Bus plunges off cliff
“An yi zargin cewa motar ce ta kubuce wa direban, inda ya yi karo da shingayen da ke kan gadar, lamarin da ya sa motar bas din ta fada gadar ta kama wuta,” in ji sanarwar.

An ci gaba da aikin ceto har zuwa cikin dare yayin da aka gano wasu gawarwakin da suka kone kurmus ta yadda ba a iya gane su, wasu kuma sun makale a cikin tarkace ko kuma suka warwatse a wurin da hadarin ya auku.

Hukumomin yankin sun ce motar bas din tana dauke da lambar motar kasar Botswana, amma ana ci gaba da tantance kasashen da fasinjojin suka fito.

Ministan Sufuri, Sindisiwe Chikunga ya je wurin da hadarin ya afku inda ya yi alkawarin za a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin.

Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashe a Afirka da ke da hanyoyi masu kyau, sai dai tana kuma daya daga cikin kasashe da mummunan hadurra ke faruwa a nahiyar.

Sa’o’i da yawa kafin hadarin, shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya yi kira ga ‘yan Afirka ta Kudu da su kula yayin tafiya a cikin makon da za a yi bikin Easter.

“Mu yi iyakacin kokarinmu don ganin an yi wannan bikin Easter lafiya,” in ji shi a cikin wata sanarwa.

Motar bas din ta fado ne daga wata babbar gada da ta hada tsaunuka biyu kusa da Mmamatlakala a lardin Limpopo, kimanin kilomita 300 (mil 190) arewacin Johannesburg.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda taron wayar da kan mata yanjarida na NAWOJ ya gudana

Next Post

Hukumar custom ta ja hankalin masu shaawar shigo da kayyaki da ketare su guji abu daya tak

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Kalli Putin yadda ya cika baki ga Amurka da kawayent

Kalli Putin yadda ya cika baki ga Amurka da kawayent

March 19, 2024
Iran Ta Ƙera Ƙwaƙwalwar Wucin Gadi Daga Kwayoyin Halittar Ɗan Adam

Iran Ta Ƙera Ƙwaƙwalwar Wucin Gadi Daga Kwayoyin Halittar Ɗan Adam

July 1, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media