DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Jami’ai a kasar Turkiyya sun ce suna ɗaukar mataki na magance duk wata matsala a ɓangaren wasannin kwallon ƙafa ta hanyar dakatar da dukkan wasu wasanni a ƙasar.
Hakan ya biyo bayan naushi da aka yi wa ɗaya daga cikin manyan alƙalan wasan ƙasar bayan wasan da aka yi a jiya Litinin.
Halil Umut Meler, ya sha naushi daga shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar ta MKE Ankaraguju, bayan sun faɗi a wasan da aka yi a gasar Super Lig Clash.
Kazalika magoya bayan ƙungiyar ma sun daki alkalin wasan wanda aka garzaya da shi asibiti don yi masa magani.
Wakilin BBC ya ce abin da ya faru a daren Litinin ya janyo tashin hankali wanda ya haɗa da ‘yan wasa da ‘yan kallo a inda aka kama mutane da dama a filin wasan.
Shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan na daga cikin wadanda suka yi alawadai da abin da aka yi.











