Jigon jami’yyar APC a Najeriya, Salihu Lukman ya caccaki jami’yyar yayin da jama’ar kasar ke cikin wani mawuyacin hali
Salihu ya ce a yanzu kokarin sabunta burin ‘yan Najeriya da Tinubu ke yi, ya sabunta kunci ne kawai a rayuwarsu
Lukman ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a Abuja inda ya bukaci gwamnati ta yi wani abu kan wahalalun da ake ciki
Lukman ya kara da cewa tsare-tsaren Shugaba Tinubu na sabunta burin ‘yan Najeriya ya sabunta musu bakin ciki ne a kasar, cewar Leadership.











