Kwanan nan aka rika yamadidin cewa sojoji sun fara shirye-shiryen hambarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta fito tayi magana a kan batun bayan sojoji sun musanta lamarin, jaridar The Cable ta bayyana.
Ministan harkokin yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris ya fitar da jawabi na musamman, yana karyata wannan magana.
Mohammed Idris ya ce ba za a janye hankalin gwamnati ko a yi mata barazanar da za ta jawo a yi watsi da gyaran da aka kawo ba.
Juyin mulki: Jawabin Ministan yada labarai “Rahoton wani bangare ne na tunanin masu neman kauda mana hankali, wadanda burinsu shi ne birkita kasar nan kuma su kawo cikas ga gwamnati mai,”
“Yanzu ya fito karara cewa wadannan daidaikun mutane sun komawa buga labaran bogi domin a cire amannar da al’umma suka yi wa gwamnati kuma su dasa tubalin rashin jituwa a kasar nan.” –
Mohammed Idris Yace Za a hukunta masu kawo maganar juyin mulki Makonni bayan hafsun tsaro ya yi magana, ministan labaran ya ce gwamnati za ta bi doka wajen casa wadanda ke wannan danyen aiki.










