• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Tarin dukiya, wata mata ta zama ta 12 a jerin wadanda suka fi kowa kudi a Duniya

aksam by aksam
December 30, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Matar da ta gaji kamfanin L’Oréal, Françoise Bettencourt Meyers ta zama matar da ta fara tara dukiyar da ta kai dala biliyan 100 (a canjin naira sun zarce tirliyan ɗaya), kamar yadda jerin lissafin mutanen da suka fi kuɗi a duniya, ya nuna.

Bafaranshiyar mai katafaren kamfanin harkar kwalliya da kakanta ya kafa, tana kan matakin nasara ne saboda harkokin hannun jarin kamfaninta tsawon shekaru gommai, suna matuƙar garawa.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Hannayen jarin L’Oréal sun yi tashin da ba a taɓa gani ba a tarihi, ranar Alhamis.

Kasuwa ta sake buɗewa ga kayan kamfanin, bayan annobar korona, lokacin da mutane ke amfani da kayan kwalliya kaɗan, saboda zaman kulle.

Tsagwaron dukiyar Francoise Bettencourt Meyers, ‘yar shekara 70, ta zarce dala biliyan 100 a jerin lissafin biloniyoyi na jaridar Bloomberg, abin da ya sa ta zama, ta 12 mafi kuɗi a duniya.

Har yanzu akwai nisa tsakaninta da takwaranta Bafaranshe Bernard Arnault, wanda shi ne na biyu a jerin masu kuɗin duniya da tsabar dukiyar da ta kai dala biliyan 179b.

Mista Arnault shi ne mai LVMH, gungun kamfanonin kayan alatu mafi girma a duniya, wanda ya mallaki kamfanonin sarrafa rantsattsun kaya masu tsadar gaske irinsu Fendi da Louis Vuitton.

Miss Bettencourt Meyers ita ce mataimakiyar shugaba a hukumar gudanarwar kamfanin. Kuma ita da ‘ya’yanta ne a dunƙule suka mallaki hannun jari mafi girma a L’Oréal da kaso kimanin 35%.

Ta kasance mai tashen da ci gadon L’Oréal daga wajen mahaifiyarta, Liliane Bettencourt, wadda ta rasu a 2017.

Liliane, wadda aka riƙa bayyana ta a matsayin matar da ta fi kowa kuɗi a Faransa, tana da alaƙa ta ƙuƙut da shugabannin ƙasar, kuma ta riƙa ɗaukar hankalin kafofin yaɗa labarai

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Harin Plateau Jam’iyar PDP ta zargi sashin fikra na jamian tsaro

Next Post

Rashin biyan Albashi jam’iyar PDP ta caccaki shugaba Tinubu

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Hukumar EFCC Na Tuhumar Wasu Ma’aurata Da Aikata Damfarar; Naira Miliyan 410.5

Hukumar EFCC Na Tuhumar Wasu Ma’aurata Da Aikata Damfarar; Naira Miliyan 410.5

December 11, 2023
Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf:-  Ya Rantsar Da Sabon Kwamashin Tsaron Cikin Gida

Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf:- Ya Rantsar Da Sabon Kwamashin Tsaron Cikin Gida

August 16, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media