Daga Hassan Umar Gwammaja
An gudanar da bikin rantsarwar ne a fadar gwamnati, inda aka bukaci sabon ministan da ya mayar da hankali kan inganta harkokin gidaje da bunkasa ci gaban birane a ƙasar.
Ana sa ran sabon ministan zai kawo sabbin tsare-tsare da za su taimaka wajen magance matsalolin gidaje da kuma samar da sauƙin mallakar gida ga ‘yan ƙasa.










