Majalisar dattawan ta musanta rahoton cewa sanatoci sun karbe tallafin kayan abinci na N200m kowanensu daga Tinubu domin rabawa talakawa
Shugaban kwamitin watsa labarai, Adeyemi Adaramodu, ya karyata jita-jitar wacce ta fito daga bakin hadimin shugaban ƙasa
Mai taimakawa shugaba Tinubu kan harkokon sadarwa na zamani ya tabbatar da cewa an fara rabawa sanatoci da yan majalisar wakilai kayan
Kana wata majiya a majalisar dattawan ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce har yanzu wasu daga cikin kayayyakin tallafin shinkafa ba su isa ga sanatoci ba.












