• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano Ta Yi Nasarar Cafke Masu Satar Kananan Yara Su Tara

aksam by aksam
December 28, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
471
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel ne, ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a shedkwatar rundunar da ke Bompai a cikin birnin Kano a yau Alhamis.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

CP Gumel ya ce, an dade ana safarar kananan yaran tare tafiya da su wasu gurare ,a fadin kasarnan, kuma rundunar ta samu nasarar ceto yara 7 daga hannun batagarin mutanen.

Tunda fari asirin wata mai suna Comfort Amos mai shekaru 45, ne ya tonu a tashar hawa motaci ta Mariri Kano, da ta ke yunkurin hawa mota domin tafiya da wani karamin yaro Abdulmutallib Sa’ad mai shekaru 5 , da aka sato daga jahar don kai shi jahar Lagos.

A wajen ne aka gano cewar yaron baya jin turanci da harshen Igbo sai yaren Hausa kawai , inda aka fara yi wa matar tambayoyi har aka cafke ta.

Sauran wanda ake zargi da safarar yaran sun hada da , Chika Ezugbu mai shekaru 52 mazauniyar Sabon Gari Kano, Joy Nzelu mai shekaru 43 sabon Gari Kano, Clement Ali shekaru 35 mazaunin Badawa Kano, Emeka Ekedigwe mai shekaru 55 mazaunin Sabon Gari Kano.

Sauran sun hada da Ruth Yarima mai shekaru 45, mazauniyar Zango Bauchi, Aner Samuel mai shekru 35 mazaunin Yelwa Bauchi, Ebere Eriobuna mai shekaru 59, mazauniyar Anambra.

Yaran da aka ceto sun hada da, Abdulmutallib Sa’ad mai shekaru 5 , wanda aka sauya wa suna Ifenyi Chukwu da aka sace daga jahar Bauchi , aka siyar dashi kan kudi naira dubu dari hudu da tamanin 480,000, sai kuma Asiya Muktar mai shekaru 4 , da aka sauya wa suna zuwa Chioma , wadda aka sato daga jahar Bauchi, aka kuma siyar da ita kan kudi naira dubu dari hudu da tamanin 480,000 da kuma Muhammad Bilyamunu mai shekaru 3, da aka sauya wa suna Chioma, wanda aka sace daga jahar Bauchi aka kuma siyar dashi kan kudi naira dubu dari hudu da hamsin 450,000.

Sauran yaran sune Usman Adamu mai shekaru 8, da aka sauya wa suna zuwa Chibuke , kuma an sato shi daga Bauchi har aka siyar dashi naira dubu dari hudu da tamanin, Hafizu Hassan mai shekaru 8, daga jahar Bauchi wanda aka sauyawa suna zuwa Uche Chukwu , aka siyar dashi kan kudi naira dubu dari hudu da tamanin 480,000, sai kuma Chiamaka Ambrose mai shekaru 7 , wadda aka sace ta , a gadon asibitin Yelwa dake jahar Bauchi bayan an haifeta , aka siyar da ita kan kudi naira dubu 300,000 na karshen shi ne Muhammad iliyasu mai shekaru 5 da aka sato daga jahar Bauchi tun yana da shekara 3 , aka kuma sauya masa suna Chidebere , har aka siyar dashi naira dubu dari biyar a jahar Anambra.

Kwamishinan yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel ya ce da zarar sun kammala za su gurfanar da su agaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Tuni dai iyayen yara suka bayyana rin cikin su , ta dagoewa rundunar an sandan jahar Kano , bisa namijin kokarin da suka yi wajen dawo da yaransu.

Yanzu haka dai yarinya daya ce kawai ake neman iyayen ta, wadda aka sace tun tana jaririya a asibitin Yelwa a jahar Bauchi, shekaru bakwai da suka gabata, amma sauran yaran duka sun hada da iyayensu.

Ko a shekarar 2019 sai da rundunar ta samu nasarar kama gungun barayin yaran su 7 tare da ceto yara 9, da ake yin sarafar su zuwa jahar Anambara kuma tuni wata babbar kotun jahar Kano ta yanke wa Poul One hukuncin daurin shekaru 104 a gidan yari sakamakon samunsa da kotun ta yi laifuka 38 da ake tuhumarsa da aikata wa na yin safarar yaran daga birnin Kano.

Share188Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kungiyar ‘Yan Majalisar Wakilan Arewa Ta Yi Allah Wadarai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Sama Da Mutane 155 A Jihar Filato.

Next Post

Al’ummar Lardin Zazzau Sun Kadu Sakamakkon Tsintar Gawar Yaro Dan Shekara 8 Mai Suna Ibrahim Kwance

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Il panorama dei giochi d’azzardo online: tra innovazione e sfide regolamentari

April 21, 2025
Gwamna Abba Kabir ya rantsar da alkalai Tara da kadi hudu

Mafi Ƙarancin Albashi: Gwamnan Kano Ya Tunawa Majalisa Karin Kasafin Kudi Domin Amincewa

August 27, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media