• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Rasha ta soma gina tashar wutar lantarki ta Sola mafi girma a Africa

Rasha ta soma gina tashar lantarki mai amfani da hasken rana mafi girma a Yammacin Afirka

aksam by aksam
May 25, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
470
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Rabin al’ummar Mali ne kaɗai ke samun wutar lantarki, ana kuma sa ran wannan aikin zai ƙara adadin lantarkin da ƙasar ke samu da kashi 10 cikin 100.

Kasashen Mali da Rasha a ranar Juma’a sun ƙaddamar da ginin tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana mafi girma a Yammacin Afirka, kamar yadda Ministar Makamashi ta Mali Bintou Camara ta bayyana a gidan talabijin na ƙasar.

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Wannan na zuwa ne a yayin da ƙasar ke ci gaba da fama da tsananin rashin wutar lantarki.

“Tashar lantarkin, wadda ita ce ta ɗaya a girma a ƙasar da kuma yankin, za ta taimaka matuƙa wurin rage matsalar ƙarancin lantarkin da ake fama da ita a ƙasarmu,” kamar yadda Camara ta shaida wa gidan talabijin ɗin Mali na ORTM.

Grigory Nazarov, daraktan kamfanin Novawind, kamfanin kasar Rasha mai kula da aikin, ya ce ana sa ran lantarkin da Mali ke amfani da ita za ta ƙaru da kaso goma cikin 100.

Shekara guda ana aiki

Novawind wani reshe ne na hukumar Nukiliya ta Rasha Rosatom.

Tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 200 za ta shafe girman kadada 314 a Sanankoroba da ke kudu maso yammacin Mali kusa da Bamako babban birnin kasar.

Aikin, wanda za a kashe sama da Euro miliyan 200 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 217, zai dauki shekara guda ana gudanar da shi, in ji Nazarov.

Sakamakon irin bashin da ya yi wa Mali katutu na sama da dalar Amurka miliyan 330, kamfanin samar da makamashi na kasar Mali ya daina samar da wutar lantarki a babban birnin kasar da sauran garuruwan kasar.

A ranar 28 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni ne aka tsara za a fara aikin gina wasu kamfanonin samar da lantarki ta hanyar hasken rana guda biyu a kusa da birnin Bamako, kuma kamfanonin China da Masar za su gina su.

Moscow ta ci gaba da samun tasiri a Mali ta hanyar tura sojojin haya na Wagner, inda take hakan a bayan fage domin biyan muradun fadar Kremlin tun daga shekarar 2010.

A yayin wata waya da suka yi a watan Maris, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da gwamnatin mulkin sojan Mali, Kanar Assimi Goita, sun tattauna kan karfafa “hadin kai a ayyukan makamashi, aikin gona da ma’adinai”, in ji Kremlin.

Share188Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda mata suka rungumi sanaar tukin Adaidaitasahu a birnin Kano

Next Post

Majalisar ministocin Burkina Faso ta tsawaita waadin mulkin Soji a kasar

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Wani jigo ya soki salon jagorancin Ganduje na jam’iyar APC

Wani jigo ya soki salon jagorancin Ganduje na jam’iyar APC

January 1, 2024

Challenges and Benefits of Gambling at handofluck casino

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media