• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kotun Daukaka Kara Dake Zamanta A Abuja Ta Soke Zaben Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna; Yusuf Liman Dahiru

aksam by aksam
November 27, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home KOTU
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA: HASSAN UMAR GWAMMAJA

Tun a ranar 30 ga watan Satumba ne Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Majalisar Dokokin Jihar ta soke nasarar da Liman mai wakiltar mazabar Makera ya samu, tare da bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 42.

RelatedPosts

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

Hakan ya biyo bayan karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Solomon Katuka, ya shigar gaban kotun yana kalubalantar zaben Liman na jam’iyyar APC.

A cikin karar da ya shigar, dan takarar na PDP ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai dangane da zaben shugaban majalisar, inda ya ce a gaskiya shi ne ya lashe zaben majalisar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023 a mazabar Makera, don haka ya kamata a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Bayanai sun ce jimillar rumfunan zabe 42 da hukuncin sake gudanar da zaben ya shafa sun hada da rumfuna 37 a unguwar Makera, da biyu a Barnawa, sai rumfar zabe daya-daya a unguwar Kakuri Gwari da unguwar Talabijin da unguwar Hausawa Kakuri.

A bisa rashin gamsuwa da hukuncin kotun, dan takarar jam’iyyar APC da kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) suka daukaka kara kan hukuncin da kotun zaben ta yanke.

Sai dai Kotun Daukaka Kara, a wani hukunci da mai shari’a O. O. Adejumo, da mai shari’a A. O. Oyetula, da kuma mai shari’a P. A. Obiora suka yanke ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba, 2023 a Abuja, ta yi watsi da daukaka karar da kakakin majalisar da INEC suka yi, tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe biyar, maimakon 42 da kotun zaben ta bayar.

Rumfunan da hukuncin sake zaben zai shafa kamar yadda Kotun Daukaka Karar ta ayyana sun hada da rumfar zabe mai lamba ta 005 da 009 a Unguwar Barnawa, da rumfar zabe mai lamba ta 006 a Unguwar Kakuri Gwari, sai rumfar zabe mai lamba ta 022 a Unguwar Television da rumfar zabe mai lamba ta 045 a Unguwar Kakuri Hausa.

A halin yanzu dai, APC na da kuri’u 17,470, ita kuma PDP ta samu kuri’u 17,088.

Kotun ta ce an soke zaben Liman ne da ya bayar da ratar kuri’u 382, wanda bai kai adadin katunan zabe da aka karba a rumfunan zabe da abin ya shafa ba.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kalli kayan kwayoyi da hukumar KAROTA ta kama ana kokarin shiga da su birnin Kano

Next Post

Kungiyar Wayar Da Kan Al’umma Kan Illar Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi Ta Masarautar Bichi Jihar Kano:- Ta Yabbawa Hukumar NDLEA

aksam

aksam

RelatedPosts

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

by Khadija Maitaya
August 7, 2026
Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar  (ADC) Na Kasa
KOTU

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

by aksam
April 30, 2026
Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin  Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa
KOTU

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

by aksam
April 30, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

by aksam
April 22, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Nadin sarauta, Sarkin Gaya ya yi wa ta Lawan abin da ya kamace su

Nadin sarauta, Sarkin Gaya ya yi wa ta Lawan abin da ya kamace su

October 9, 2023
Tsananin Zafi Ya Halaka Ɗaruruwan Alhazai A Hajjin Bana A Saudiyya

Tsananin Zafi Ya Halaka Ɗaruruwan Alhazai A Hajjin Bana A Saudiyya

June 20, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media