• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Wata Kotun A Jihar Kano Ta Tura Amarya Da Angonta Gidan Yari

aksam by aksam
May 3, 2025
Reading Time: 2 mins read
0
Home KOTU
ADVERTISEMENT
471
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

Daga: Hassan Umar Gwammaja

Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta tura wata mata da sabon mijinta gidan yari na tsawon mako guda, bayan ta amsa cewa ta yi aure a kan aure

Kotun da ke zamanta a Post Office, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Munzali Tanko Soron Dinki, ta yanke wannan hukunci ne bayan jin karar da wani magidanci ya shigar, yana zargin matarsa da yin aure da wani mutum duk da cewa bai sake ta ba.

Aksam Medio  ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a unguwar Tudun Murtala da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, lokacin da mijin ya kai ziyara gidan matarsa, inda ya iske wani mutum kwance a gadonta.

A cewar sa, sai da ya tambaye su matsayin su, inda matar ta ce mutumin da ke gadon dan uwanta ne. Amma daga bisani sai mijin ya gayyato makota suka zo suka shaida abin da ke faruwa, kafin ya garzaya kotu domin shigar da kara.

A gaban kotu, mijin ya bayyana cewa har yanzu yana da aure da matar, kuma har kwana biyu da suka gabata suna tare da ita. Sabon mijin kuwa ya ce matar ta fada masa cewa ba ta da aure, kuma ya biya sadakinta na Naira dubu 100 kafin a daura auren.

Lokacin da kotu ta tambayi matar ko za ta rantse cewa tsohon mijin nata ya sake ta, sai ta ce ba za ta iya rantsewa ba. Haka kuma ta hana tsohon mijin daga rantsewa cewa har yanzu suna da aure.

Daga nan ne kotu ta bukaci jami’an tsaro su tafi da su. A lokacin, matar ta ce za ta fadi gaskiya. Sai ta bayyana wa kotu cewa hakika ta yi aure a kan aure, sannan ta nemi gafara.

Mai Shari’a Munzali Tanko Soron Dinki ya ce wannan laifi ne mai tsanani a shari’ar Musulunci, sannan ya bayar da umarnin a tura su gidan gyaran hali na tsawon mako guda domin horo da nazari.

Share188Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kamfanin GYAZUWA Carpentry Solution yafito da sabuwar hanyar dadada wa abokan hulɗar sa

Next Post

Yadda Aka Buɗe Makarantar Koyon Wanki Da Guga A Asibitin AKTH 

aksam

aksam

RelatedPosts

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

by Khadija Maitaya
August 7, 2026
Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar  (ADC) Na Kasa
KOTU

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

by aksam
April 30, 2026
Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin  Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa
KOTU

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

by aksam
April 30, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

by aksam
April 22, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Il ruolo crescente dei Giocatori Italiani nel Football Online: un’analisi approfondita

April 21, 2025

Uwar jam’iyyar APC ta kano ta dauki tsatstsauran mataki kan wadanda suka dakatar da Ganduje

April 16, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media