Gwamnatin tarayya ta karbi ƴan Najeriya kimanin 103 da aka kawosu daga kasar Turkiyya bisa dalilai da suka hada da ƙarewar biza da shiga ƙasar ba bisa ka’ida ba.
Kwamishinan hukumar kula da ƴan gudun hijira da bakin haure ta kasa (NCFRMI) Alhaji Tijani Ahmed ne ya bayyana haka a jiya Juma’a, a lokacin tantance waɗanda aka koro din a Abuja.
Ahmed, wanda darakta mai kula da al’amuran hijira a hukumar Amb. Catherine Udida, ya wakilta, ya ce hukumar ta yi tsammanin za a aiko mutane 110 amma sai ta karbi 103, dukkansu maza.
“Wasu daga cikinsu sun shafe watanni a sansanin waɗanda aka koro, kuma yanzu da suke nan, muna fatan za mu bi diddigin duk wasu zarge-zargen da aka rubuta a kundin bayanansu.
Za mu bi ta fom din tantancewa, saboda wasu sun ce an kwace fasfo dinsu.
“Za mu bi diddigin hukumomin Turkiyya, saboda har yanzu fasfo mallakin Tarayyar Najeriya ne,” in ji shi.











