Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, ya ce karin harajin da aka yi a baya-bayan nan na VAT wata manufa ce ta Gwamnatin Tinubu da za ta ƙara jefa tattalin arzikin ƴan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Atiku ya ce Tinubu tare da mashawartan sa sun kuduri aniyar kara kuɗin harajin VAT daga kashi 75 cikin 100 zuwa kashi 10 cikin 100 a kuma dai-dai lokacin da kamfanin Man Fetur na Najeriya (Nigerian National Petroleum Company Limited NNPCL) ya sanar da karin farashin litar Mai.
Dan Takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata a cikin sakonsa na dandalin X da ya wallafa a ranar Lahadi ya ce, matakin ya bayyana wani sabon zamani na siyasar kama karya da kuma azabtarwa da shuwagabanni suke yiwa ƴan ƙasa.
A cewarsa tasirin ƙarin harajin na VAT da na Man Fetur zai ƙara ta’zzara tsadar rayuwa ga ƴan Nijeriya da kuma ƙara tabarbarewar ci gaban tattalin arzikin Najeriya da tuni ya riga da ya samu matsala











