Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta ba matasa masu shirin zanga-zanga damar gudanar da ita cikin lumana ba tare da matsala ba
Rundunar ta bukaci duka kungiyoyin da ke cikin zanga-zangar su ba da bayansu da na shugabanninsu a hukumance
Babban Sifetan ƴan sanda, Kayode Egbetokun shi ya tura bukatar inda ya ce hakan zai ba su damar dakile bata-gari a cikin shirin
Egbetokun ya ce sun dauki wannan mataki ne domin tabbatar da gudanar da zanga-zangar cikin kwanciyar hankali,
Babban Sifetan ya ce hakan ne zai ba su damar zakulo bata-gari da ke son kawo cikas a shirin zanga-zangar.












