Daga Hassan Umar Gwammaja
Kakakin Hukumar Saminu Yusif Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar ‘yan jaridu a yammacin yau Jumu’a, inda ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Danbare Daura da Amana City, Dake karamar Hukumar Kumbotso.
A cewar sa, “Da misalin karfe 9:24 na safiyar yau Jumu’a ne muka sami kiran neman agajin gaggawa, ta wani hannun wani mutum Bashir Salisu, inda ya sanar da mu fadawar wata Matashiya cikin Rijiya, lamarin da ya sanya muka tura jami’an mu daga Shelkwatar hukumar domin ceto ta”.
Bayan sun je sun sami nasarar ciro ta ne suka tarar ta rasu, mafari kenan da suka damka ta a hannun Dagachin Garin Danbare Malam Magaji Kasim.
Toh sai ‘Yan uwan Marigayiyar sun tabbatar da cewa tana da lalurar tabin hankali, wanda kuma Matashiya ce ba ta taba yin aure ba, amma hukumar ta ce tana kan binciken musabbabin faruwar wannan Iftila’i.










