An Halaka Tsohuwa da Jikarta a Katsina
Labari ya ishe mu cewa wasu miyagu da ba’a san ko suwaye ba sun shiga har cikin gida sun halaka wata tsohuwa da jikarta a garin Daura da ke jihar Katsina.
Legit ta ruwaito cewa Miyagun maharan sun halaka mutanen ne a cikin wani yanayi mara daɗi bayan sun yi musu kutse cikin gidansu.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar mai shekara 90 a duniya an halaka ta ne ta hanyar shaƙewa
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ƙatsina ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike












