An yi kira ga Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta taimakawa alummar mazabar giginyu dake karamar hukumar Nassarawa, bisa wata gada da ake tsallakawa da tayi sanadiyyar mutuwar mutane da ma musamman kananan yara da Kuma gyara Tsohon Asibitin Badawa wanada ya dade babu gyara.
Sakataren jamiyyar APC Kuma Shugaban kungiyar Giginyu Peace Kwamared Isah Ado Muhammad Badawa ne ya yayi wannan Kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a sakonsa na barka da sallah.
Sakataren jamiyyar yace gyara Tsohon Asibitin da gyaran gadar zai taimaka gaya wajen ragewa alummar yankunan matsalolin da suke fuskanta na rashin Asibitin da za su rika zuwa domin Neman lafiya.
Isah Ado Muhammad Badawa ya bayyana cewar, alummar badawa dake karamar hukumar Nassarawa, mutane ne da suke baiwa Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf hadin Kai a kodayaushe wajen ganin siyasarsa ta Kara bunkasa Inda yace, duk inda Gwamnan Kano yake suna tare da shi.
Shugaban kungiyar Giginyu Peace Kwamared Isah Ado Muhammad Badawa ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf akan yadda yake baiwa kungiyar Giginyu Peace cikakken hadin Kai da goyan baya yadda ya kamata domin inganta alummar yankunan.
Haka zalika, Shugaban kungiyar Kuma Sakataren jamiyyar APC na mazabar giginyu Isah Ado Badawa ya jaddada kudirinsa na ci gaba da baiwa Jamiyyar APC karkashin jagorancinsa Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf cikakken hadin Kai domin ganin an ciyar da jihar Kano gaba, musamman a wannan lokacin da Gwamnatin ta take tunkarar manyan zabuka na Shekarar 2027 dake tafe.
Sakataren jamiyyar APC ya Kuma taya Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf da “ya jamiyyar APC da Alummar jihar Kano murnar karamar sallah.
Sakataren jamiyyar ya baiwa Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf tabbacin cewa, kungiyarsa ba za ta gajiya ba wajen Gwamnatin gudunmawa ba domin cimma kudirin da ta sanya a gaba ba.











