Ministan Harkokin Wajen Saudiyya ya kammala ziyararsa a ƙasar China a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwar siyasa tsakanin shugaban Amurka, Donald Trump, da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman (MBS).
Rahotanni sun nuna cewa Saudiyya na ci gaba da nazarin illolin tsaro da yaƙe-yaƙen yankin suka haifar, tare da faɗaɗa dangantakarta da ƙasar China domin ta zama wata madogara ta diflomasiyya a matsayin daidaito ga tasirin United States, da kuma abokiyar hulɗa wadda za ta iya taka rawa wajen mu’amala da Iran.
Wannan mataki na nuni da yadda Saudiyya ke ƙoƙarin ƙarfafa alaƙarta da manyan ƙasashe daban-daban domin tabbatar da tsaro da kuma kare muradunta a yankin Gabas ta Tsakiya.












