Yadda gobara ta ƙona masallaci tare da ɗaiɗaita mutum 120 a Kwara
Wata gobara da ta tashi a ƙaramar hukuar Ilori ta Kudu a jihar Kwara ta ɗaiɗaita mutum 120 tare da ƙona ɗakuna 44 na wani gini da masallaci.
Shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar kashe gobara, Hassan Adekunle ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin a Illorin, babban birnin ƙasar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito jami’in yana cewa hukumar kashe gobara ta jihar ta kai ɗauki zuwa gidan Megida Onikanhun a ƙaramar hukumar Illorin ta Kudu.
“Masu kashe gobara da isar su sun ga wuta ta laƙume ginin baki ɗayansa saboda an yi kiran wayar a makare.” a cewar sa.
Ya ce masu kashe gobarar sun rushe katangar ginin domin samun damar kashe gobarar yadda ya kamata.
A cewar snarwar, bincike ya nuna cewa wani mutum ne ya kyasta wa shara wuta inda aka yi rashin sa’a wutar ta mamaye ginin.
Mr Adekunle ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa zuwa wakilin Magaji Megida Onikanhun, Kuranga Adebayo.
Ya kuma yaba wa jami’an kashe gobarar sai dai ya ce wutar ta ɗaiɗaita mutum 120 har da masallaci amma kuma ba a samu asarar rai ba a ginin mai ɗaki 75.
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Falade Olumiyiwa ya buƙaci jama’a da su ama masu taka tsan-tsan musamman a yanayin da ake ciki na hunturu.











