Kasar China ta sanar a ranar Litinin cewa ta kakaba takunkumi kan kamfanonin Amurka guda 10 masu alaka da harkokin tsaro da soja. Matakin ya zo ne a matsayin martani ga sabuwar dokar Amurka da ta hana wasu manyan kamfanonin fasahar China shiga kwangilolin tsaro da na sojin Amurka.
Mahukuntan China sun bayyana cewa kamfanonin da aka sanyawa takunkumin za su fuskanci ƙuntatawa wajen gudanar da harkokinsu a cikin kasar, ciki har da zuba jari, hada-hadar kasuwanci da sauran ayyukan kasuwanci. Beijing ta ce matakin ya zama dole domin kare muradun kasa da kuma mayar da martani ga abin da ta kira matakan rashin adalci daga Washington.
A baya-bayan nan, gwamnatin Amurka ta kafa sabbin dokoki da ke hana wasu kamfanonin fasahar China shiga ayyukan da suka shafi tsaro da kwangilolin soja. Jami’an Amurka sun ce an dauki wannan mataki ne domin kare tsaron kasa da kuma rage yiwuwar samun barazana daga kamfanonin kasashen waje a muhimman shirye-shiryen tsaro.
Sabuwar musayar takunkuman ta nuna yadda takaddama tsakanin China da Amurka ke ci gaba da tsananta kan batutuwan fasaha, kasuwanci da tsaro. Masana sun yi gargadin cewa ci gaba da daukar irin wadannan matakai na ramuwar gayya na iya kara dagula alakar kasashen biyu tare da yin tasiri ga kasuwannin duniya, zuba jari da tattalin arzikin kasa da kasa.
A Dangane da wannan sa-toka-sa-katsi shirin Duniya Makaranta ya taba alli da masanin harkokin diflomasiyya kuma Mai fashin bakin Bash M Bash kan ko Hakan ka iya sauya wasu lamura kan ƙasar ta Amurka
Kamfanoni 10 da China Ta Kakaba Wa Takunkumi
Kamfanoni 10 da China ta sanya wa takunkumi sun haɗa da AVEOX da ke birnin Simi Valley na jihar California; Red Cat Holdings da Teal Drones, waɗanda dukkansu ke South Salt Lake a jihar Utah; da kuma IMSAR da ke Springville, Utah.
Sauran kamfanonin sun haɗa da Jaia Robotics da ke Bristol a jihar Rhode Island; Ball Aerospace & Technologies da ke Broomfield, Colorado; da Oshkosh Defense da ke Oshkosh, Wisconsin.
Har ila yau, takunkumin ya shafi L3Harris Maritime Services da ke Norfolk, Virginia; MP Materials da ke Las Vegas, Nevada; da kuma USA Rare Earth da ke Stillwater, Oklahoma.











