Ƙasashen yankin Gulf irin su Saudiyya da Kuwait sun ƙi bai wa Amurka damar amfani da sararinsu da sansanoninsu bayan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da wani shiri mai suna “Project Freedom” domin tabbatar da tsaron mashigin ruwan Hormuz.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin da waɗannan ƙasashe suka ɗauka ba wai saboda goyon baya ga Iran ba ne, sai dai saboda tsoron martanin da Tehran za ta iya mayarwa idan rikici ya ɓarke a yankin Gulf. Mashigin Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin safarar man fetur a duniya.
Masana harkokin siyasa sun ce ƙasashen Gulf na ƙoƙarin kauce wa shiga rikicin kai tsaye tsakanin Amurka da Iran, musamman ganin yadda yankin ya taɓa fuskantar barazanar tsaro a lokutan tashin hankali tsakanin ɓangarorin biyu.
Wannan lamari na nuna yadda ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya ke ƙara taka-tsantsan wajen hulɗa da manyan ƙasashen duniya, yayin da ake ci gaba da fargabar cewa duk wani sabon rikici zai iya kawo cikas ga tattalin arziki da tsaron yankin baki ɗaya.












