Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO mai kula da jihohin kano katsina da jigawa ya bayyana cewa a gobe Lahadi 29 ga watan October, zasu dauke wutar daga karfe 7 na safe zuwa Karfe 7 na yamma.
Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a dare ranar Asabar din nan.
“Muna sanar da kwastomomin mu cewa zamu dauke wuta a gobe Lahadi domin baiwa kamfanin TCN damar gudanar da wasu aikace-aikace akan layin da ya kawo wutar daga Kaduna zuwa Kano”.
Sanarwa tace TCN zasu gudanar da aikinne na sauyawa wasu turakunsu wuri sakamakon aikin layin dogo ( Titin jirgin kasa) da ake yi daga Kaduna zuwa Kano.
Kamfanin ya bukaci al’ummar Kano da su yi hakuri saboda tsaikon da za’a samu, amma ya bada tabbacin cigaba da yin duk mai yiyuwa don kyautatawa abokan huldar su.












