Kungiyar jami’an tsaro na sa Kai ta kasa reshen jihar Kano ta jaddada aniyarta na ci gaba da samar da cikakken tsaro a dukkannin fadin kasar nan.
Jami”in Hulda da jama’a na kungiyar S. A.Usma Abdullahi Umar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Manema labarai a ofishinsa dake nan jihar Kano.
Usman Abdullahi Umar yace jami’nsu karshin jagoranci shugaban Kungiyar Alh Abdullahi Al’amin suna taka mahimmiyar rawa ba da cikakken tsaro ba wai kawaii a jihar Kano ba,har ma da sauran sassan kasar nan.
Ya bayyana cewar, ya kamata Gwamnatin tarayya da ta jihohi su yi duba na musamman da za’a sanya jami’in tsaro na sa Kai cikin tsarin biyan albashi na din-din-din domin suna dogara da kawunansu da inganta rayuwarsu da ta iyayensu.
Yace jami’nsu suna man Akan barkarsu na ci gaba da samar da cikakken tsaro da kare lafiya da dukiyoyin alummar musamman a wannan lokacin da muka samu kanmu a ciki na kwacen wayoyin alumma da matasa suke yi Yanzu, Wanda wannan ba karamar matsala brace.
Baya ga haka ya bayyana cewar Kungiyar tana Jan ragamar Kungiyar ne da dan wani Abu kalilan Wanda, yakamata Gwamnatoci a matakai daban daban da zo su taimakawa Kungiyar bisa Yadda suke sadaukar kawunansu domin tsaron al’umma.
Yace lokaci yayi da Gwamnatin tarayya Ko ta jihohi za su sanya Kungiyar jami’an tsaro na sa Kai cikin tsarin biyan albashi kamar Yadda ake biyan kawanne jami’in tsaro da Kuma Samar musu kayayyakin aiki da za su gudanar da ayyukan su, yin hakan zai taimakawa gaya wajen Kare lafiya da dukiyoyin alummar.
Daga karshe yayi Kira ga jami’an sa kai, da su kara zage damtse wajen gudanar da ayyukan su tare da basu tabbacin cewa, Shugabanninsu na kasa suna nan suna kokari na ganin an sanyasu a cikin kyakyawan tsarin biyan albashi da samar da kayayyakin aiki da biyasu alawus-alawus da zai taimakawa aikinsu.
Ya Kuma shawarce su da su kiyaye kwarai da gaske wajen ganin sun kare hakkokin wanda aka zalinta Ko za’a zalunta, Inda yace yakamata su kiyaye dokokin da Kungiyar jami’an tsaro su ta dorasu a kai domin Ka da wani ko wata su kuka da su saboda Kungiyar ba za ta laminci irin wannan ba.
Ibrahim sani Gama radio Nigeria pyramid









