An bayyana cewa Cikin Yan majalissun jahar kano goma Sha shida na yankin kano ta kudu,daya ne yabi kawu sumail
Tsohon wakilin kananan hukumomin takai da sumaila a majalissar tarayyar Nigeria, Kuma mashawarci ga gwamna jahar kano engr Abba Kabir Yusuf a maaikatar kananan hukumomi,hon Garba Umar Durbunde ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa dake maaikatar,
Yace fitar kawu sumaila daga jamiyar NNPP ba zai zama barazana ga jamiyar ba kasancewar irin yadda alumar kano ke cin gajiyar mulkin balaraben gwamna wajen sharbar romon damakaradiyya da aiyukan raya kasa da ake ta bujuro dasu dan inganta rayuwar jama,a,
Hon Durbunde yace sanata kawu bashi ne mutum na farko daya fara yiwa madugu butulci ba Dan haka bazai hana cin zabe a jahar kano ba domin shi kadai ya fita bada aluma ba.












