Gwamnatin Kano ta biya kuɗin makarantar daliban da tayi alkawari
Gwamnatin jihar kano ta ce ta kammala biyan kuɗin makaranta ga dalibai ‘yan asalin jihar dake karatu a jami’ar Bayero Kano.
Sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Kabiru Haruna Getso ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai
Yace gwamnatin ta biya akalla Naira Miliyan 700 ga dalibai sama da dubu bakwai domin su sami damar cigaba da karatun su.
” Dama gwamnan Abba Kabir Yusuf yayi alkawarin biya musu kudin yau talata cikin iKon Allah ya cika wannan alkawari, don haka ɗaliban da abun ya shafa zasu iya zuwa jami’ar domin Kara cike-ciken da suka dace don cigaba da karatun su”. A cewar Kabiru Getso
Sakataren zartarwar ya kuma yabawa gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya damu da ganin matasan jihar kano sun sami Ilimi mai inganci don kyautata rayuwar su.












