Daga Musa Mudi Dawakin Tofa
DETFund: Ya Raba Tallafin Kayan Koyarwa ga Makarantu 22, a Dawakin Tofa.
Asusun Tallafawa Ilimi na Dawakin Tofa (Dawakin Tofa Education Trust Fund DETFund) ya gabatar da taron raba tallafin kayan koyarwa ga makarantu biyu-biyu daga mazabu 11 a karamar hukumar, don kara bunkasa harkokin ilimi, a ranar Asabar 11/01/2025.
Shugaban kwamatin kula da asusun DETFUND Dr Junaidu Dalladi ya ce an samar da asusun ne a karkashin kulawar kungiyar Malaman Makarantun Gaba da Sikandire ‘Yan Asalin Karamar Hukumar Dawakin Tofa (Dawakin Tofa Academic Forum DAF), tun a shekara ta 2023, don taimakawa da bunkasa harkokin ilimi a ciki da wajen karamar hukumar.
“… Tun bayan da kungiyar DAF ta samar da kwamatin wannan shi ne karo na biyu da asusun ya raba tallafin kayan koyarwa ga makarantu 22 dake karkashin hukumar kula ilimin bai daya ta Dawakin Tofa”.
“… An raba katan 3 na kwallin alli da littafin rubutu 40 da littafin adana bayanan koyarwa 4 da rigistar kiran suna 4 ga kowacce makaranta”.
“… Ya yi kira ga sauran al’umma da su rika bada tallafinsu don kara ciyar da harkokin ilimi gaba a karamar hukumar”.
Shugaban kungiyar DAF Associate Professor Engr. Mamunu Mustapha Imam ya godewa duk mutanen da suka sanya tallafinsu a cikin asusun don ganin an kara bunkasa harkokin ilimi a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Sakataren ilimin hukumar bai daya ta Dawakin Tofa Malam Ahmad Shu’aibu ya yabawa kokarin kungiyar DAF kana ya yi kira ga makarantun da suka amfana cewa sun yi amfani da tallafin ta hanyar da ta dace da kuma sanyasu a inda suka dace.
Shugaban kwamatin bada tallafin karatu na karamar hukumar Dawakin Tofa Malam Abdullahi Mijinyawa ya bukaci kungiyar DAF da ta fadada neman tallafin DETFund ga sauran al’umma musammanma masu daukar albashi.
Sakataren gidauniyar ilimi ta Sale Kuidawa Malam Lawan Usman Dawaki ya yi alkawarin cigaba da baiwa kungiyar DAF hadin kai akodayaushe, kana ya bukaci kungiyar da ta rika rubutawa shugaban gidauniyarsu sakon neman taimako a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Kansilan riko a sashen Ilimi na karamar hukumar Dawakin Tofa Honarabul Muhammad Ahmad da hedimastoci 22 na daga cikin wadannan suka halarci taron raba tallafin DETFund, a cikin dakin taro na cibiyar gudanar da harkokin addinin Musulunci dake Dawakin Tofa a jihar Kano.










