Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya yi barazanar fallasa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da kuma jagoran kwankwasiya, Santa Rabiu Musa Kwankwaso, “a lokacin da ya dace.”
A karon farko tun bayan da aka cire shi daga mukaminsa tare da wasu kwamishinoni biyar a watan Disamba 2024, Bichi ya yi magana kan abin da ya faru, inda ya yi zargin cewa akwai wasu bayanan sirri da ya tanadar a kan shugabannin biyu.
Da yake jawabi ga magoya bayansa a ranar Alhamis, bayan dawowarsa daga Saudiyya, Bichi ya ce ya na da takardu, murya, da bidiyo da za su tabbatar da abin da ya ke zargi. Ya bayyana Kwankwaso da Yusuf a matsayin shugabanni masu yaudara da rashin amana.
Ya ce:
“Na yi farin ciki da na kammala wa’adin aikina lafiya. Amma kamar yadda kuka sani, wannan ba shi ne lokacin da ya dace don magana ba. A lokacin da ya dace, za mu fallasa su don al’umma su gane irin mutanen da suke. Ba mutane masu amana ba ne… suna cike da yaudara da cin amana.”
Bichi ya kara da cewa:
“Mun rubuta komai kuma mun tanadi dukkan shaidu daga rubuce-rubuce zuwa na murya da bidiyo.”
Kafin saukarsa daga mukamin SSG, jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da shi bisa zargin rashin biyayya ga shugabancin jam’iyyar. An rahoto cewa Bichi ya samu sabani da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, bayan ya jagoranci wata kungiyar siyasa ta sirri mai suna “Abba Tsaya da Karka,” wadda ke neman Abba Yusuf ya rabu da Kwankwaso.











