Gwamnatin Najeriya ta ce ta rage farashin buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 da kashi 50 zuwa N40,000 a fadin kasar.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a karshen taron majalisar zartarwa da aka yi ranar Litinin 29-07-2024 a Abuja.
cewarsa, rage farashin shinkafar ya zo ne a daidai lokacin da aka tura motocin dakon kaya 20 ga gwamnonin jihohi daban-daban domin rabawa ‘yan Najeriya.
Ya ce sun kuma rage farashin Shinkafar da kusan kashi 50 na kudinta ga yan Nigeria, tuni an tura Shinkafar wurare daban-daban a jihohin kasar nan domin sayar da ita akan farashin naira dubu 40. An samar da cibiyoyi, ta yadda masu bukatar wannan shinkafa za su je can su saya a kan Naira 40,000,” inji shi.












