Dan majalissar wakilai mai wakiltar hukumomin kiru da Bebeji Hon Abdulmumin jibrin kofa ya sauke nauyin daya daukarwa daliban na yankin kiru da bebeji, nabasu tallafin karatu na naira miliyan goma (10,000,000) domin rage musu dauniyar karatun da kuma kara musu kwarin gwiwar cigaba da karatun nasu taron bada tallafin wanda ya gudana a gidan sa dake nan kano.
Yayin ya yake mika check din kudin mun jiyo Hon Abdulmumin jibrin kofa yana cewa wannan tallafin somin tabu ne idan daliban zasu hade kansu da sauran mambobin su to kafar shi a Bude take wajen cigaba da tallafawa dalibai tunda daman wannnan abune wanda ya saba kullum
Taron dai ya samu halartar jiga jigan mutane a fannin ilimin da kuma dattawan yankin na kiru da babeji da Suka hadar da farfesa Shehu Tajjani, HOD. Economics BUK, Sai kuma farfesa Nasir T. Dabo kiru Dept of medical microbiology, BUK,
Sai kuma farfesa Mahraz bebeji – Dept, Geography BUK, NUT chairman kiru, Aminu A lawan da kuma NUT chairman na Bebeji, muhd Ashiru kofa, wakilan kungiyoyin Dalibai na kiru da bebeji da sauran Dattawan yakin.












