A tsakiyar wannan mako ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa wasu Dalibai daga cikin waɗanda za su amfana da shirin bayar da rancen kudin karatu takardar samun bashing da suka nema, a ɗakin taro na fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Shirin, wanda ake kira NELFUND a turance, an fito da shi ne domin taimaka wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi samun rancen kuɗi domin kammala karatunsu, inda za su biya bayan kammala makaranta, in ji shugaban asusun, Jim Ovia.
Ya kuma bayyana cewa yawan mutanen da suka nemi karɓar bashin ya zuwa yanzu sun zarce 110,000 sannan kuma sama da mutum 160,000 ne suka ziyarci shafin neman karɓar bashin.
Bashin nawa za ku iya ci?
Yawan bashin da za a bai wa ɗalibi ya danganta ne da yawan kuɗin makaranta da kake biya, kasancewar bashin ba zai je ga aljihun ɗalibi ba.
Asusun bayar da bashin karatun zai biya makarantar da kake karatu isassun kuɗaɗe ne da za su isa a bar ɗalibi ya halarci darussa, rubuta jarrabawa da sauran abubuwan da suka shafi karatu.
Baya ga kudin makaranta, asusun bayar da bashin karatun zai kuma biya ɗalibi wasu ƴan kuɗaɗe da zai riƙe a hannu domin samun damar rayuwa a makaranta.
Asusun bai sanar da yawan kudin da zai bai wa ɗalibi a hannunsa ba, sai dai shugaban asusun ya ce kuɗaɗen a ƙayyade suke.
Yadda za ka nemi bashin karatu
Akwai matakai haɗu da ake bi wajen tura buƙatar neman bashin karatu na NELFUND.
Matakan su ne:
A ziyarci shafin Nelfund.
Yin rajista a shafin Nelfund ta hanyar shiga wurin da aka rubuta “APPLY NOW”.
A danna wurin tura buƙatar neman bashi “Request for Student Loan” domin cike fom.
A cike fom ɗin neman bashin sai a tura “Submit”.
A cikin fom ɗin da za a cike zai buƙaci mutum ya cika sunan makarantar da yake, da lambar karatu (matriculation number) da kuma ɗora takardun karatu.
Haka nan za ka bayyana matakin da kake na karatu.
Mun a nan tafe da yadda ake biya da kuma abubuwan da zasu Hana ka samu











