Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa wani jirginta maras (UAV) ya yi hatsari a kusa da ƙauyen Rumji da ke cikin jihar Kaduna.
Wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar ta hannun daraktanta na yaɗa labaru, Edward Gabkwet ta ce jirgin ya samu matsala ne jim kaɗan bayan tashi daga filin jirgi.
Sanarwar ta ƙara da cewa “kasancewar jirgin maras matuƙi ne, babu wanda abin ya rutsa da shi a sama ko a ƙasa”.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an fara bincike domin gano abin da ya faru.
Kuma sanarwar ta musanta labaran da ke cewa wani jirgin soja ne mai saukar ungulu ya yi hatsarin.











