• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda dubun wani barawon yara ta cika cif bayan sace wata yarinya tare da kulle ta a firji

aksam by aksam
April 30, 2024
Reading Time: 1 min read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Wani wanda ake zargin barawon mutane ne ya sace wata yarinya ’yar shekara 10 ya boye ta a cikin firinji a shagonsa a Jihar Kaduna.

Rundunar ’yan sanda a jihar ta ce jami’anta sun kama wanda ake zargi da sace yarinyar.

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan, ya ce ranar Asabar, da misalin karfe 2 na rana ne Huwaila Idris mahaifyar yarinyar da aka sace a Unguwar Gara da ke karamar hukumar Kauru ta kawo musu rahoton bacewar diyarta.

ASP Mansir Hassan, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) a ranar Talata cewa mahaifiyar yarinyar “Ta kai wa ’yan sanda rahoton cewa a ranar 26 ga Afrilu, da misalin karfe 1 na rana wani mai shago da ke unguwarsu ya sace ’yarta mai shekaru 10 mai suna Hanifa a lokacin da ta je shagonsa.

“Bayan nan ne ya rufe bakinta da Hijabi, sannan ya sanya ta cikin firinji ya kulle ta a ciki da kwado”.

Bayan dawowarsa ne wasu matasan unguwar suka ce ba su yarda ba sai sun bincike shagon.

“Samarin yankin sun dage cewa sai sun bincike shagon, suna cikin binciken ne suka gano Hanifa a kulle a cikin firinji a shagon.

“Zuwa yanzu dai wanda ake zargin yana hannu kuma ana ci gaba da bincike domin gano dalilin aikata wannan mummunan aiki,” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna.

Hassan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

NNPCL ya ambata waadin da zai kawo karshen laying man fetur

Next Post

Wani gwamna ya mayar da mafi karancin Albashi Naira 70,000 a jihar sa

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano
LABARAI

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

by Abdulhamid Isa
September 7, 2026
Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Kotun Daukaka Kara Dake Zamanta a Abuja Ta Tabbatar Da Nasarar Zaben Gwamna Bala Muhammed Na Jihar Bauchi

Gwamna Bala Mohammed Na Jihar Bauci; Ya Ce Idan Jonathan Zai Dawo Takara 2027 To Zai Jan Ye Masa

August 16, 2024
A shirye muke wajen ganin kananan hukumomi sun dawo cikin hayyacinsu,

Gwamnatin Jihar Kano Ta Sassauta Dokar Hana Fita Daga;-

August 3, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Babban mataki na kawar Da Matsalar Tsaro A Jihar Kano

September 7, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media