Hukumar Hana fasakwauri ta kasa shiyyar kaduna ta yi alwashin cigaba da dakile shigowa da kayayyakin da doka ta hana zuwa kasar nan.
Jami’in hukumar mai kula da shiyyar zone B da ta hada kaduna da Katsina, kwanturola Dalha Wada Chedi ya sanar da hakan a ganawar sa da manema Labarai a jawabin sa na ayyukan da hukumar ta gudanar daga watan Fabrairu zuwa karshen wannan wata na Maris da muke ciki.
Ya ce a tsawon wannan lokaci hukumar ta samu nasarar kama kayayyaki daban-daban na miliyoyin Nairori da aka shigo da su kasar nan ba bisa ka’ida ba.
Comptroller Dalha Wada Chedi ya ce jami’an hukumar na aiki babu dare babu rana wajen cigaba da aiki wajen dakile shigowa da kayayyakin da basa bisa doka kasar nan musamman a wannan lokaci da kungiyar ECOWAS ta bakin Shugaban kasa Bola Tinibu ya bayar da umarnin bude iyakokin Najeriya da Nigir
Ya Kuma Ja hankalin Al’uma da su kauce wa wannan dabi’a ta shigowa da kayayyakin da basa bisa doka kasar nan kasancewar akwai doka da ka’idoji da aka Samar da suka kamata kowa ya bi idan yana bukatar shigowa ko Kuma fitar da kaya kasar nan.
Chedi ya Kuma yaba wa sauran Jami’an tsaro bisa yadda suke tallafawa hukumar domin samun nasarar ayyukan ta.











