Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta sami nasarar kama motoci guda hudu kirar J5 maqare da giya
Shugaban Hukumar KAROTA Hon. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a daren jiha
Lokacin da yake duba motocin bayan da jami’an Hukumar suka sami nasarar cafke motocin
Ya ce Hukumar KAROTA ta sami nasarar kama motocin ne bayan rahoton sirri da ta samu a wajen wasu masu kishin jihar Kano
Ya ce dokar jihar Kano ta haramta shan giya a ko wanne lokaci, musamman yanzu da ake cikin wata mai alfarma
Ya kara da cewa Ya zama wajibi Hukumar ta rubanya kokarinta wajen sa ido a daukacin titinan jihar Kano.
A karshe ya yabawa jami’an da suka sami nasarar cafke motocin. Ya ce da zarar an kammala binciki za a mika Giyar Hukumar Hizba domin ta kara fadada bincike tare da daukar mataki na gaba
Signed
Nabilusi Abubakar
K/Na’isa
P.R.O KAROTA
27/3/2024.












