Gwamnatin Jihar Borno ta buƙaci al’ummar jihar su yi azumi a ranar Litinin 19 ga watan Fabrairu, domin neman sauƙin ubangiji dangane da tsadar kayan abinci da fashewar abubuwa a wasu manyan titunan jihar.
Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi kafar yaɗa labaran jihar.
“Ina magana da ku a yau cikin tsananin takaici, amma ina da yaƙinin cewa za mu iya magance matsalolin da ke addabar jiharmu”, na damu matuƙa da halin matsin rayuwa da al’ummar jiharmu ke fuskanta, musamman tsadar kayan abinci”, in ji Zulum.
Gwamnan ya ci gaba da cewa a gwamnatance suna ɗaukar matakan da suka dace don magance matsalar.












