Kotun shari’ar addinin Muslunci dake zaman ta a hukumar hisbah ta jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Malam Sani Tamim Sani Hausawa, ta yanke wa Shahararriyar yar TikTok din nan mai suna Ramlat Muhammad da aka fi sani da princess hukuncin daurin watanni 7 a gidan yari .
Mai Shari’a Malam Sani Tamim yace kotun ta sami Ramlat Muhammad wadda akewa lakabi da Princess da laifin badala, fitsara da kuma yawon banza.
A yammacin ranar litini 19 ga Fabrairu na 2024, Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa ya yanke wa Ramlat hukuncin dauri na tsawon watanni bakwai da zabin biyan tarar Naira 50,000.
Nuna fitsara da rashin tarbiyya da yada ɓaɗala, da yawon tazubar wanda ya saba da sashe na 389 na dokar Shari’ar Musulunci ta jihar kano.
A tuhumar farko alkalin ya yanke wa Ramlat hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku ko zabin tara ta Naira dubu talatin.
Sai laifin yawon banza, wanda a kansa alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata uku a ko zabin tara na Naira 20,000.
A laifi na uku da aka kama ta da shi na fitsara kuma alkalin ya yanke mata hukunci bisa sassauci da ta nema zaman gidan yari na tsawon wata guda babu zabin tara.
Idan za’a iya tunawa dama tun a hannun jami’an hukumar Hisbah ta jihar kano Ramlat ta amsa laifinta tare da neman ayi mata sassauci.










