DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Ya bayyana haka ne a yayin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai a cikin garin Bauchi, ya kuma ce wannan lokacin tsayawar takarar na matasa ne, kamar yadda “Yan iya magana kance; matasa sune manyan gobe” A dan haka ya kamata abawa matasan Jihar Bauchi dama domin su gwada irin tasu basirar, musammam idan aka kulla da godimawar da suke ba gwamnatin zabebban gwamna Jihar Bauchi Sanata Dakta Bala Muhammad ton farkon farar milkinsa har izuwa yau
Hon. Sunusi Talba Duguri, yace dolane mu matasa mu jinjinawa Uwargidan gwamna Jihar Bauchi kuma Amaryar gwamna da Shugaban jam’iyar PDP na Jihar da kuma Shugaban Hukumar Kulla Da tsaro na jihar (SSS).










