Al’ummar jihar Legas sun bi sahun jihohin da aka gudanar da zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da tsadar rayuwa a ƙasar nan.
A Legas, mata da matasa ƴan kasuwa sun yi zanga-zanga a unguwar Ibeju-Lekki da ke jihar Legas a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu, a cewar rahoton Daily Trust.
Sun ɗauki kwalaye masu rubuce-rubuce irin su “Baba Tinubu, ƴan Nijeriya suna jin yunwa” da ‘Tinubu, ka zo ka cece mu’ da dai sauransu, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Zanga-zangar ita ce ta baya-bayan nan a jerin zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Kogi da Osun da Neja da kuma Kano kan tsadar rayuwa a ƙasar nan. Tun bayan cire tallafin man
Tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar nan.
Wannan tsadar kayayyakin tare da faɗuwar darajar Naira ya sanya an shiga halin matsi a cikin Najeriya, inda mutane ke kokawa kan yadda rayuwa ta yi matuƙar tsada.











